Kasuwanci
Farashin Kayan marmari ya tashi a Kano bayan fara azumi
Mutane da dama na yin amfani da kayan marmari lokacin azumi sabanin yadda suka saba a baya.
Sai dai mutane na kokawa kan yadda a duk irin wannan lokaci akan samu farshin kayan ya yi tashin gwauron zabi.
masu sayar da kayan na kara musu farashi
A Tattaunawa gidan Radiyon Freedom da wani mai sayar da kayan marmari a kasuwar Yan Lemo da ke Na’ibawa a nan kano Malam Ali Yabanya, ya ce, a yanzu haka buhun lemo ana sayar da shi akan naira dubu goma sha biyu zuwa dubu goma sha hudu.
Ya kara da cewa, an samu karanci Ayaba a kasuwar inda ya ce bai sayo ta ba saboda tsadar da ta yi.
Ya bayyana farashin Gwanda Dozin guda a kan naira dubu bakwai da dari biyar sai kuma Kankana Kwallo guda daga naira dari biyar zuwa sama.
Ali Yabanya ya kuma ce, a na sayar da Kwallon Abarba guda daya daga naira dubu daya da dari biyar zuwa sama.
Shi kuwa a nasa bangaren Malam Gali Abubakar mai sayar da Mangwaro a kasuwar ta Yan Lemo ya bayyana cewa an sayar da Kwalli guda akan naira dubu shida zuwa dubu bakwai.
You must be logged in to post a comment Login