Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Farashin Kayan marmari ya tashi a Kano bayan fara azumi

Published

on

Mutane da dama na yin amfani da kayan marmari lokacin azumi sabanin yadda suka saba a baya.

Sai dai  mutane na kokawa kan yadda a duk irin wannan lokaci akan samu farshin kayan ya yi tashin gwauron zabi.

masu sayar da kayan na kara musu farashi

A Tattaunawa gidan Radiyon Freedom da wani mai sayar da kayan marmari a kasuwar Yan Lemo da ke Na’ibawa a nan kano Malam Ali Yabanya, ya ce, a yanzu haka buhun lemo ana sayar  da shi akan naira dubu goma sha biyu zuwa dubu goma sha hudu.

Ya kara da cewa, an samu karanci Ayaba a kasuwar inda ya ce bai sayo ta ba saboda tsadar da ta yi.

Ya bayyana farashin Gwanda Dozin guda a kan naira dubu bakwai da dari biyar sai kuma Kankana Kwallo guda daga naira dari biyar zuwa sama.

Ali Yabanya ya kuma ce, a na sayar da Kwallon Abarba guda daya daga naira dubu daya da dari biyar zuwa sama.

Shi kuwa a nasa bangaren Malam Gali Abubakar mai sayar da Mangwaro a kasuwar ta Yan Lemo ya bayyana cewa an sayar da Kwalli guda akan naira dubu shida zuwa dubu bakwai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!