Connect with us

Labaran Wasanni

CAF CHAMPIONS: Dole sai mun zage dantse wajen kaiwa zagaye na gaba-Kennedy Boboye

Published

on

Mai horos da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Akwa United Kennedy Boboye, ya ce dole sai kungiyar ta kara zage dantse wajen ganin ta kai zagaye na gaba a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafar Afrika CAF.

A ranar Lahadi 12 ga watan Satumbar shekarar 2021 da muke ciki ne dai kungiyar kwallon kafar ta Akwa United ta doke kungiyar CR Belouizdad a gasar da ci 1-0.

Wikki: Mun shirya tunkarar kakar wasanni mai zuwa -Balarabe Douglas  

Mai horos da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar ta Akwa United Kennedy Boboye, ya ce duk da cewa sun sami nasara a wasan, amma akwai bukatar dagewa ga ‘yan wasan kungiyar.

A minti na 87 ne dai kungiyar kwallon kafa ta Akwa United ta zura kwallon da ta bata nasara.

Kungiyar kwallon kafa ta Akwa United da Enyimba da kungiyar kwallon kafa ta Bayelsa United da kuma Rivers United sune suke wakiltar Nigeria a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin Afrika na Champions league da kuma gasar  Confederation cup.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!