Kiwon Lafiya
CBN ya sanya wa’adin shekaru 5 ga bankuna kafin su lalata duk cakin da abokan huldar su suka gabatar musu
Babban bankin kasa CBN ya sanya wa’adin shekaru biyar ga dukkanin bankunan kasar nan kafin su lalata dukkanin wani cakin kudi da abokan huldar su suka gabatar musu domin karbar kudi.
Wannan na kunshe cikin wata sabuwar dokar tantance lamuran kudi da babban bankin ya fitar a jiya, a cewar bankin wannan sabon tsari zai taimaka wajen samar da nagartaccen aikin banki a kasar nan.
Wannan doka dai ta yi dai-dai da tsarin dokokin da ikon da doka ta baiwa babban bankin kasar a sashi na 2 (d) da na 33 (1)(b) na shekarar 2007 domin inganta harkokin kudi a kasar nan.
Wannan sabuwar doka da babban bankin kasar ya fito da ita wacce ta fara aiki nan take, ya ce dukkanin bankin da ke da lasisi, kuma baya cikin wannan tsari to lallai ya shiga domin bin wannan doka ta adana chakin kudin.