Labaran Wasanni
Chelsea ta lashe gasar Club World Cup
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta zama zakara a shekarar 2022 a gasar cin kofin kungiyoyin kasashen duniya na FIFA Club World Cup.
A karon farko da kungiyar tayi nasarar lashe gasar, bayan kaiwa ga karin minti 30 wato extra-time, inda sukai nasara akan tawagar da ke Brazil wato Palmeiras.
A minti na 17 ne dai dan wasa Kai Havertz ya zura kwallon da ta baiwa kungiyarsa nasara, fafatawar da ta gudana a ranar Asabar 12 ga Fabrairun 2022, a birnin Abu Dhabihadaddiyar daular larabawa.
Ko a gasar cin kofin zakarun turai na shekarar 2021 dan wasan Kai Havertz ne ya zura kwallon da kungiyarsa ta Chelsea yin nasara akan Manchester City da ci daya da nema.
Nasarar da Chelsea tayi ya sa ta lashe ko wacce gasa a duniya karkashin jagorancin shugaban kungiyar Roman Abramovich.
Tinda fari dan wasa Romelu Lukaku ne ya fara zura kwallon farko a wasan, kafin dan wasa Raphael Veiga ya warware kwallon da aka zura.
You must be logged in to post a comment Login