Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Wani mai kutse ya sace dala dubu arba’in a asusun Neymar

Published

on

‘Yan sanda a kasar Brazili sun kama wani mutum da ake zargi da yin kutse har mada sace kudi da suka kai yawan Dala dubu ar’ba’in a asusun dan wasan kasar Neymar JR.

Rahotannin da kafar sada zumunta ta kasar ta Sao Paulo ta fitar sun bayyana cewa ‘yan sandan suna zargin mutumin da yin kutse a wani banki da dan wasan har mada mahaifinsa keyin ajiyar kudi.

“Tuni muka samu nasarar kama matashin mai shekara 20 a ranar Laraba, bayan zarginsa da yin kutse a bankin da bana shi ba, a cewar sanarwar da ‘yan sandan kasar suka fitar.

Neymar JR

Sai dai ‘yan sandan basu fadi sunan matashin da ake zargi ba, sakamakon bin cike da ake ci gaba da yi akansa.

Sai dai mai magana da yawun dan wasa Neymar Lopes bai ce komai ba kan lamarin lokacin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tuntube shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!