Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Chelsea ta lashe gasar Club World Cup

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta zama zakara  a shekarar 2022 a gasar cin kofin kungiyoyin kasashen duniya na FIFA  Club World Cup.  

A karon farko da kungiyar tayi nasarar lashe gasar, bayan kaiwa ga karin minti 30 wato extra-time, inda sukai nasara akan tawagar da ke  Brazil wato Palmeiras.

A minti na 17 ne dai dan wasa Kai Havertz ya zura kwallon da ta baiwa kungiyarsa nasara, fafatawar da ta gudana a ranar Asabar 12 ga Fabrairun 2022, a birnin  Abu Dhabihadaddiyar daular larabawa.

Ko a gasar cin kofin zakarun turai na shekarar 2021 dan wasan  Kai Havertz ne ya zura kwallon da kungiyarsa ta Chelsea yin nasara akan Manchester City da ci daya da nema.

Nasarar da Chelsea tayi ya sa ta lashe ko wacce  gasa a duniya  karkashin jagorancin shugaban kungiyar Roman Abramovich.

Tinda fari dan wasa Romelu Lukaku ne ya fara zura kwallon farko a wasan, kafin dan wasa Raphael Veiga ya warware kwallon da aka zura.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!