Kiwon Lafiya
Cibiyar AHIP ta bayyana damuwa kan karuwar cin zarafin ‘dan-adam da ke karuwa a Kano
Wata Cibiya mai rajin tallafawa rayuwar Iyali da dakile cin zarafin bil’adam ta AHIP, ta bayyana damuwarta kan karuwar cin zarafin ‘dan-adam da ke karuwa a Jihar Kano.
Babban jami’in tsare-tsare na cibiyar Malam Abba Bello Ahmad ne ya bayyana hakan, ta cikin shirin Mu Leka Mu Gano na musamman na nan tashar Freedom Rediyo.
Malam Abba Bello Ahmad, ya bayyana cewa, adadin cin zarafin da ke karuwa a Jihar nan ya hadar da na sabani a tsakanin Iyali, tare da cin zarafin kananan yara musamman ma ‘ya’ya mata, wanda hakan ke neman zama ruwan dare a halin yanzu.
Haka zalika ya kara da cewa, kunya da boye laifin masu aikata cin zarafin yaran da aka yi wa fyade na daga cikin dalilan da ke janyo karuwar aikata laifukan, sakamakon kin tona asirin wadanda aka kama.
Ya kuma ce, rashin koyar da yara wasu daga cikin hanyoyin da za su kare kansu daga fadawa hannun bata-gari da iyaye ke yi, na taka rawa wajen kara haifarwa yaran matsala.
Malam Abba Bello Ahmad ya bayyana cewa, samar da hukunci mai tsanani kan wadanda aka kama da laifin cin zarafin yara musamman ma fyade, hakan zai taimaka matuka wajen dakile yaduwar aikata laifin fyaden.