Labarai
Cibiyar CAJR ta horar da matasa 60 kan wanzar da zaman lafiya a jihar Filato
Cibiyar wanzar da adalci da kare hakkoki ta CAJR ta horar da mata da matasa 60 a matsayin masu ba da shawara ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma.
Babbar Daraktar cibiyar ta CAJR Miss Etty Peter ta ce an gudanar da taron bayar da horon ne ga al’ummar karamar hukumar Barkin Ladi dake jihar Plateau.
Ta ce, Hukumar bunkasa kasashen duniya ta kasar Amurka wato (USAID) ce ta dauki nauyin shirin karkashin jagorancin shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya (NERI).
Ta kuma bayyana cewa, shirin ya kuduri aniyar hada kan al’ummomin da suka rabu da juna sakamakon rikice-rikicen a aka yi shekaru da dama tsakanin Fulani makiyaya da ‘yan asalin Berom.
Peter ta ce an zabo mahalarta taron daga garuruwa uku da ke cikin karamar hukumar, kuma za su koyar da darussan da aka koya musu a wasu sassan jihar.
You must be logged in to post a comment Login