Kiwon Lafiya
Cibiyar CISLAC ta bayyana damuwar ta kan kamun da ‘yan sandan SARS ke yiwa ‘yan jarida
Cibiyar da ke kula da ayyukan yan majalisu CISLAC ta bayyana damuwar ta kan yawan karuwar kama yan jarida da jami’an sashen kula da manyan laifuka na SARS ke yi duk kuwa da sauya musu fasali da aka yi a baya-bayan nan.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ta Alhaji Auwal Ibrahim Musa, inda ya ce hakan da jami’an SARS ke yi babban abin takaici ne.
Haka kuma cibiyar ta yi kira ga jami’an tsaro da su rika tabbatar da bin doka da oda kafin gudanar da aikin su musamman ma kame mutane.
Cibiyar ta CISLAC ta kuma jaddada bukatar da ke akwai wajen yiwa jami’an yan sanda karin girma a dai-dai lokacin da ya kamata.
Sannan kuma cibiyar ta bayyana rashin tabbatar da tsarin nan na kwarmata bayanan masu satar dukiyar kasa a matsayin abinda ka iya kawo koma baya ga ci gaban shari’o’i a kasar nan.
Daga nan kuma sai cibiyar ta ce koda a bangaren zaben masu shari’a akwai bukatar gyara duk don tabbatar da samun shari’a ta adalci kuma cikin gaggawa.