Labarai
Cin hanci da rashawa ne ke haifar da koma baya a Najeriya – Dr. Dukawa
Masanin kimiyyar siyasa nan na jami’ar Bayero da ke nan Kano, Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin babban abinda ke haifar da koma-bayan al’amura a Najeriya.
Dakta Dukawa ya bayyana haka ne yau jim kadan bayan kammala shirin ‘Barka da Hantsi’ na nan tashar Freedom Rediyo da ya mayar da hankali kan matsalar dakatar da tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa ta kasa, EFCC, Ibrahim Magu.
Ya bayar da shawarar daukar matakin gyara yadda hukumar ta EFCC ke gudanar da ayyukanta tare da sabunta dokokin da suka kafata don ba ta damar gudanar da ayyukan ta ba tare da yi mata katsalandan ba.
Wani dan kungiyar kwadago, Malam Isa Tijjani da ya kasance cikin shirin, cewa ya yi abu ne mai kyau idan shugaban kasa, Muhammad Buhari ya yi magana kan lamarin kasancewar shine ke da damar yin wani abu a kan matsalar don yi masa saiti.
Ya ce mafi yawan rigingimun da ake fama da su a kasar nan cin hanci da rashawa ne ke haddasa su.
You must be logged in to post a comment Login