Manyan Labarai
Cin zarafin Fulani makiyaya babu abinda zai janyo sai kara rura wutar rikici- Hassan Kukah
Shugaban Cocin Katolika shiyyar Sokoto Mathew Hassan Kukah, ya ce, cin zarafin Fulani makiyaya babu abinda zai janyo sai kara rura wutar rikici tsakanin al’ummar kasar nan.
Rabaran Mathew Hassan ya bayyana hakan ne yayin wani taro kan dakile labaran kire da furta kalamai da ke tunzura jama’a; wanda sashen nazarin nahiyar afurka, a cibiyar Olusegun Obasanjo ta jami’ar karatu daga gida ta shirya a Abuja.
Mathew Hassan Kukah ya kara da cewa, furta kalamai da ke tunzura jama’a, ya taka rawa wajen janyo kisan kiyashi a sassa daban-daban na duniya.
Ya ma buga misali da yakin basasan Najeriya wanda ya ce irin wadannan kalamai shi ya ta’azzara rikicin da yayi sanadiyar hallaka miliyoyin al’ummar kasar nan.
Shugaban Cocin na Katolika shiyyar Sokoto, ya kuma ce, ba da wanna shawara ya zama wajibi sakamakon farfagandar da ke biyo bayan duk wani lamari na rashin tsaro da ke faruwa a kasar nan yanzu, inda ake alakntashi da Fulani batare da gudanar da cikakken bincike kan lamarin ba.