Manyan Labarai
Cin zarafin mata yana karuwa a Najeriya
Majalisar dinkin duniya ta ce, har yanzu cin zarfin ya’ya mata na kara karuwa a sassa daban-daban na duniya.
Hakan na cikin wani rahoto ne da hukumomi daban-daban na majalisar ta dinkin duniya suka fitar kan rayuwar mata a duniya.
Rahoton da aka fitar a jiya laraba, ya nuna cewa a Najeriya an yiwa mata miliyan goma sha tara da dubu dari tara kaciya.
Rahoton wanda hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF da hukumar kula da al’amuran mata wato UN WOMEN da wata kungiyar kasa da kasa mai suna Plan International suka fitar, sun bukaci kasashen duniya da su kara kaimi wajen yaki da matsalolin cin zarafin ‘ya’ya mata.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, a kalla ya’ya mata milyan goma sha uku ne a sassa daban daban na duniya ne aka ci zarafinsu wajen yi musu fyade ko tursasu yin mu’amala da maza duk kuwa da cewa, shekarunsu ba su kai ba.
You must be logged in to post a comment Login