Kiwon Lafiya
Citad: bude shafukan boge da sunan shugabanni na kara yada kalaman batanci
Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma CITAD ta ce yawan bude shafukan sada zumunta na bogi da wasu mutane ke yi da sunan manyan mutane na taimakawa wajen yada kalaman tunzuri a cikin al’umma.
Jami’in da ke kula da sashen tattara alkaluman kalaman batanci a shafukan sada zumunta Hamza Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da cibiyar ta gudanar yau Talata a nan Kano.
yayin taron dai cibiyar ta gabatar da litattafai kala 3 da ta rubuta kan kalaman batancin da ta tattara a daga shekarar 2017 bara 2018 musamman bangaren addini da siyasa da kabilanci tare da bude shafuka na boge.
Malam Hamza Ibrahim ya kuma ce sun gudanar da binciken ne kan jihohin Kano da Jigawa da Kaduna da Plateau sa Niger da Nassarawa da Bauchi da Gombe da kuma jihar Adamawa wanda.
Ya kuma ce a watan Fabrairun shekarar nan da muke ciki cibiyar ta gano cewa gwamnan Jihar Kano Datka Abdullahi Umar Ganduje yana da shafukan sada zumunta guda 168, yayin da gwamnan jihar Kaduna Nasir El’Rufa’i ke da shafuka 225 shi kuma dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ke da guda 4 yayin da Malam Salihu Sagir Takai ke da 8 baya ga wasu manyan mutane.