Kiwon Lafiya
Citad ta wayar da kan matasa kan yadda za su sami cigaba a rayuwar su
Tsohon shugaban hukumar kula da ‘yancin dan Adam ta kasa Farfesa Muhammad Tabi’u ya shawarci matasa dasu maida hankali wajen rungumar tsarin da zai kaisu ga cimma manufofin sun a ci gaban rayuwa.
Farfesa Muhammad Tabu’u na sashen shari’ar musulunci dake jami’ar Bayero anan Kano ya bayyana hakan ne yayin taron dake nusar da matasa harkokin shugabanci da cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma ta CITAD ke shiryawa wata-wata.
Ya ce ya zama wajibi matasa su dauki ta’adar shugabanni nagari don fuskantar matsalolin da suka dabai-baye tattalin arziki da ci gaban kasa baki daya.
daraktan cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma ta CITAD Yunusa Zakari Ya’u ya ce manufar shirin shine don fadakar da matasa yadda za su fuskanci kalubalen rayuwa tare da yin nasara kan abubuwan da suka saka a gaba.