Labarai
CITAD ta yi tsokaci kan kudirin yaki da kalaman batanci
Cibiyar fasahar sadarwa da cigaba al’umma ta CITAD ta bukaci al’ummar kasar nan da su bi hanyar laluma kan batun kudurin dokar nan ta dakile
ayyukan sada zumunta da kalaman batanci a shafukan sada zumunta ke gaban majalisar dattijan kasar nan, don samun damar janye batun.
Wannan kira ya fito ta bakin babban daraktan cibiyar Yusha’u Zakari Ya’u, cikin wata sanarwa da ya fitar jiya aka rabawa manema labarai.
Ta cikin sanarwar, Yusha’u Ya’u ya bayyana cevwa gabatar da kudurin wani yunkuri ne tauye hakkin al’ummar kasa da ke neman an aivwatar da
shugabanci cikin gaskiya da adalci kuma a bayyane, tare da girmama doka da hakkin dan adam.
Ya kara da cewa daga cikin masu goyon bayan kudurin akwai jami’an tsaron kasar nan da ke cin zarafin al’umma a wuraren da ke da shingen bincikeen ababen hawa suna gallaza musu, har ma suna kashe wasu, inda suke kamawa tare da daure mutane ba tare umarnin Kotu ba, ka na kuma suna bijirewa umarnin Kotu, inda suke da muradin samun kariya don ci gaba da muzgunawa al’umma.
Cibiyar CITAD ta ja kunnen fasinjoji kan kula da kayan su a filayen jirage
Cibiyar nazarin harkokin tsaro za ta koyar da matasa sabbin dabarun tsaro
Citad: bude shafukan boge da sunan shugabanni na kara yada kalaman batanci
Daraktan cibiyar ya ce akwai dokokin da aka yi tanadi don hukunta masu
yada kalaman kiyayya da batanci, wadanda matukar aka aiwattar da su yadda ya kamata to za su magance matsalolin da ake fuskanta a shafukan sada zumunta.
Haka zalika ya bayyana cewa kudurin ya sabawa sashe na 39 na kundin
tsarin mulkin kasar nan, a don haka ne ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nesanta kasa da kudurin don kare martabar Dimokradiyyar kasar nan.