Coronavirus
Corana : Ba a kawo mana yara rigakafi ba-ma’aikatan jinya
A yayin da aka kwashe watanni shida da bullar cutar Covid 19 a kasar nan, wani ma’aikacin jinya da ya nemi a sakaye sunansa a nan Kano, ya ce, a watanni ukun farko da aka samu bullar wannan cutar an samu karacin masu karbar rigakafin kananan yara a asibitocin jihar Kano.
Ma’aikacin jinyar ya ce, a watanni ukun farko da cutar ta bulla, cikin watannin Maris da afrilu, da kuma Mayu, iyaye basa kai ya’yansu riga kafin, sakamakon tsoron daukar cutar Covid 19 a asibiti.
Ya kara da cewa, a watannin Yuni da Yuli zuwa watan da ake ciki na Agusta, an samu karuwar masu zuwa karbar rigakafin.
Wakiliyarmu Shamsiyya Farouk Bello ta rawaito cewa an samu fitowar mata da yawa, sabanin farkon watannin da aka samu bular cutar ta Covid 19.
You must be logged in to post a comment Login