Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Corona Virus : An ki cin Biri an ci Dila

Published

on

Tun bayan bullar Murar mashako ta Corona Virus a karshen  Disambar shekarar data gabata a birnin Wuhan na kasar Sin wato China, zuwa yanzu haka annobar na kara fantsama fadin duniya inda yanzu haka sama da mutum dubu dari uku ne suka kamu da ita ,tare da mutuwar sama da dubu sha shida a fadin duniya.

Kasashe da dama, da hukumomi daban-daban,  attajirai , ‘yan wasa, dai -dai kun mutane da dubban likitoci da masana na ta bada gudunmowa ta fannoni daban -daban don ganin cewar an shawo kan wannan annoba da ta gagari Kundila.

Cutar wacce ake daukar ta ,ta hanyar yin mu’amala tsakanin al’umma kana mai saurin yaduwa ta cikin iskar da dan adam yake shaka tana bukatar taka tsan tsan da matakai daban -daban da masana kiwon lafiya suka bada shawarwari wajen rage yaduwar ta ,ciki har da killace kai da zama waje daya ba tare da mu’amala cikin dubbun nan jama’a ba.

Zuwa yanzu haka kama daga Saudi Arabia, Hadadiyar Daular Larabawa (UAE), Qatar, Amurka, Italiya  sun dau matakan rufe manyan gurare na Ibada, harkokin yau da kullum, makarantu, da guraren shakatawa da duk wani nau’i da zai hada cunkoson jama’a, tare da umartar al’ummar kasashen da kowa ya zauna a gida hukumomi zasu cigaba da biyan sa kudade da kuma samar musu da abubuwan bukatu na yau da kullum.

Tun bayan bullar cutar a kasar nan da wani dan kasar Italiya ya shigo da ita a jihar Lagos, cutar na kara yaduwa a fadin kasa wanda a yanzu haka ana da yawan mutum 46,  da suka kamu da cutar ciki har da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Malam Abba Kyari da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad sai dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, wato Muhammad Atiku.

Kamuwar wadannan mutane wanda kusan manyan turaku ne ko kuma mu kira su ‘Wuta da Batir ‘ ma’ana masu karfin iko ko fada aji da yadda zasu yi , ya sa shakku da tambayoyi a zukatan al’ummar kasar nan.Shin ina makomar kasar nan ,ma iya cewa kaikayi koma kan mashekiya ke nan ?

Wasu daga cikin tambayoyin da ke dar suwa a zukatan jama’a ke nan.In har gwamna guda mai rike da madafun iko da shugaban ma”aikatan fadar gwamnatin tarayya mai matukar iko da dan tsohon shugaban kasa mai matukar tasiri da wadata, zasu kamu , a ce a fadin kasa babu cikakkun kayan aikin da za’a kula dasu a Abuja, Bauchi da Adamawa, babu kuma damar fita zuwa kasashen ketare sakamakon killace kasashen  su da tsoron shigo musu da cutar ma iya cewa kaikayi ya koma kan mashekiya sakamakon shuwagabanni sun gaza wajen sauke nauyin dake wuyan su na yiwa al’umma hidima da samar musu da abinda yake a hakku kuma wajibi a matsayin su na ‘yan kasa.

Kama da ga sha’ani na lafiya ,Noma ,Ilimi da wutar lantarki ,tatalin arziki, kasuwanci, hanyoyi, tsaro na rayuka da dukiyoyin al’umma da makaman tansu zamu iya bada maki sifiri ga jagororin da suka rike a baya da wanda suke rike da kasar nan a yanzu sun gaza kwata -kwata ,illa iyaka kaurin suna wajen wasoson dukiyar talakawa da ajiye ta a asusun kasashen duniya da ba zai amfani al’ummar kasar nan ba.

A ya yinda wasu rahotannin sirri na bincike dangane da kadarorin da wasu ‘yan kasar nan suka mallaka a birnin Dubai, da ake zargin ta  hanyar yiwa tattalin arzin kasa zagon kasa da wasoso da dukiyar al’umma suka mallaka, wanda kudaden sun isa bunkasa kasar nan da wadatacciyar wutar lantarki ta dun -dun-din, tare da samar da ingantaccen harkokin kiwon lafiya  da cire kashi saba’in cikin dari na al’ummar kasar nan da ke fama da talauci , a gefe daya kayan agajin yaki da Cutar mai lakabin Covid 19, na  Attajirin da yafi kowa arziki dan kasar China Jack Ma, da ya taimaka wa kasashen duniya ciki har da kasar nan, sun sauka don cigaba da yakar cutar da takaita yaduwar ta.

Kowanne lamari yana zuwa da alfanu ko akasin sa, in har akwai yiwuwar killace al’umma da hanasu zirga -zirga ko fita neman na yau da kullum , shin wane tanadi hukumonin da suka kasa samar musu da kayan aikin inganta lafiyoyin su suka tanadar musu kasancewar su da ni sai mun fita kullum sannan mu samu  ‘yar tsabar da zamu kai baki ?Ina masu arzikin mu , mai suka tanadarwa al’umma a wannan hali na tsanani da ake ciki in har Jack Ma , zai taimaka tun daga kasar Sin ?Ma iya cewa alfanun cutar Corona, ya fara haskakawa shuwagabannin mu  son kan su da matsalolin su da rashin adalcin da suka dade suna yiwa al’ummar kasar nan.Fatan  mu a samu dalilai da zasu hana masu rike da  madafan iko samun mafaka, ajiye dukiya, neman lafiya ko wasu uzurin ba gaira ba dalili a kasashen Nahiyar Turai da Amurka ko kasashen da suka bunkasa ta dalilin jagoranci na gari.

Zuwa yanzu dai lamarin ya zama kaikayi koma kan mashekiya, kuma kukan kurciya da muke fatan jawabin yaje ga kunnen su , don kuwa lokaci ya yi da za  su karkato da tunanin  su wajen bunkasa kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!