Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Fiye da mutane 40,000 ne suka mutu a hatsarin mota cikin shekara 1- FRSC

Published

on

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Nijeriya FRSC ta ce, sama da mutum dubu 40 ne suka mutu cikin shekara guda sakamakon hadarurruka daban-daban a fadin kasar.

Babban jami’i a hukumar, Dauda Ali Biu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da makon kiyaye hadura na Duniya da ake gudanarwa a kowacce shekara.

Yayin kaddamar da makon kiyaye hadura da majalisar dinkin duniya ta ware daga ranar 15 zuwa 21 ga watan Mayun ko wacce shekara, Babban jami’in hukumar ta FRSC  Malam Dauda Biu ya ce, raunikan da ake samu idan an yi hatsari shi ne ke janyo ajalin dubban mutane tare da jikkatar wasu.

Haka kuma ya kara da cewa, mutane miliyan daya da dubu dari uku ne ke rasa rayukan su yayin da wasu miliyan 50 kuma ke jikkata sakamakon hadari a fadin duniya.

Dauda Biu, ya kuma ce, akwai bukatar ci gaba da daukar matakan inganta hanyoyi domin kare rayukan mutane a fadin duniya.

 

Rahoton: Ummulkhairi Abubakar Ungogo

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!