Connect with us

Labaran Kano

Covid-19: Rundunar ‘yan sandan Kano ta dakatar da karbar korafi baka-da- baka

Published

on

Rundunar yansandan Jihar Kano ta ce za ta rinka karbar korafin da yazamo dole ne kawai ta wayar Salula domin kaucewar yaduwar cutar Korona a fadin jihar Kano.

Komishinan Yansandan Kano CP Habu Ahmad Sani, ne ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Kano DSP Abdullah Haruna, a yayin zantawarsa da wakilin mu Abba Isah Muhammad, a shelkwatar rundunar dake Unguwar Bomfai a nan Kano.

Abdullahi Haruna, ya kara da cewar sun dauki wannan mataki ne domin yaki da yaduwar cutar korona.

DSP Abdullahi Haruna, ya kuma kara da cewar idan ya zamo dole sai mutum ya kawo korafi kafa da kafa to wajibi ne yazo shi kadai maimakon gayyato abokansa.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa Rundunar ‘yansandan ta Jihar Kano ta sallami wandanda ake zargi da aikata kananan laifuka ta hanyar bayar dasu beli zuwa wani lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,693 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!