Connect with us

Coronavirus

Karin mutum 23 sun kamu da Coronavirus a Kano

Published

on

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta ce mutane 23 ne suka kamu da cutar Coronavirus a Kano ranar Litinin.

Sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce yanzu Kano tana da mutane 59 da suka kamu da cutar an samu karin mutane 38 da suka kamu da cutar ranar Litinin a sassa daban-daban Najeriya.

Jihar Kano ce kan gaba a yau Litinin da ta samu karin mutane 23 sai jihar Gombe da ta samu mutane 5, jihar Kaduna ta samu karin mutum 3 sai jihar Borno da ta samu karin mutum 2, ita ma jihar Abia ta samu mutane 2 birnin tarayya Abuja ta samu karin mutum 1 Sokoto ta samu mutum 1 sai jihar Ekiti ita ma an samu karin mutum 1.

Har ila yau hukumar ta NCDC ta ce a ranar Litinin din adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya ya kama 665 inda mutum 188 suka warke, mutane 22 kuma suka mutu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,754 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!