Connect with us

Coronavirus

Covid-19: An janye dokar kulle a Ringim

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da dage dokar kulle a karamar hukumar Ringim ta jahar jigawa sakamakon nasarar da ake samu wajen yaki da cutar a jihar.
Shugaban kwamatin karta-kwana na dakile yaduwar cutar Covid-19 a jihar Jigawa Dakta Abba Umar ne ya bayyana haka da yammacin Alhamis din nan.
Dakta Abba yace an dage dokar ne a garin Ringim da kuma sabon Garin Yaya ta karamar hukumar Taura samakon rashin yaduwar cutar zuwa ga wasu tun bayan mutane na farko a garuruwan da aka samu na dauke da cutar ta corona Virus.
Haka kuma Dakta Abba ya kara da cewa, akwai wasu gwaje-gwajen mutane da ake jiran fitowar su, kuma shi ne zai haska makomar garuruwan Gwaram da Birnin Kudu na yiwuwar a dage musu dokar kokuma aci gaba da zaman gida.

Labarai masu alaka:

An gano karin mutane 14 dauke da cutar Covid-19 a Jigawa

Covid-19: Cibiyar gwajin Corona zata fara aiki a Jigawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,753 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!