Connect with us

Labaran Kano

Ana zargin jami’in lafiya da yiwa bazawara fyade a Kano

Published

on

Kotun shari’ar musulunci dake zamanta a garin Madobi dake nan Kano ta cigaba da shari’ar jami’in ladiyar nan Sani Dahiru wanda ake zargi da yiwa wata bazawara fyade.

Tun da farko wata bazawara mai suna Fatima Yusuf ce tayi karar Sani Dahiru, bisa zargin ya hilace ta ya zuba mata wani sinadari mai juyar da tunani acikin shayi.

Bayan ta sha shayin ne, sai bacci ya kwashe ta, shi kuma yayi lalata da ita.

Sai dai a lokacin da taji alamun juna biyu sai taje asibiti domin a duba lafiyar ta, sai ta iske Sani Dahirun shi ne mai duba marasa lafiya a asibitin, daga nan ne kuma sai ya bata wani magani, sannan yace da ita ciwon sanyi ne yake damun ta, ya sallame ta.

Bayan tasha maganin ne, sai ya haifar mata da sabuwar wahala ta dan loakaci, domin kuwa ashe maganin zubar da ciki ne.

Wakilin mu Yakubu Musa Kanwa ya rawaito mana cewa Fatima Yusuf tayi sabon aure, a nan ne kuma sabon mijin ya gane tana da juna biyu sannan ya sallameta.

A yayin zaman kotun na jiya Talata wanda ake zargi Sani Dahiru ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.

A don haka alkalin kotun mai shari’a Bello Musa Khalid ya dage wannan shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Afrilu mai kamawa, tare da umarnin ajiye wanda ake zargi a gidan gyaran hali.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Addini

Za ayi zubeben kwarya tsakanin malaman Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce nan bada jimawa da zarar wucewar annobar Covid-19 za ta shirya wata gagarumar Mukabala a tsakanin bangarorin addini dake jihar, domin kawo karshen gutsiri-tsoma dake faruwa a tsakanin su.
Kwamishinan al’amuran addini na jihar Kano, Malam Muhammad Tahar Baba Impossible shi ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da wakilin mu Yusuf Ali Abdallah a yau Laraba.
Baba Impossible yace, biyo bayan takun saka da ake yawan samu kan batanci ga addini tare da wuce gona da iri daga wasu al’umma, ya sanya daukar wannan mataki domin rarrabewa da baccin makaho.
Har ila yau, Impossible ya ce, a kwanakin baya jami’an tsaron farin kaya DSS sun gayyaci dukkan bangarorin malaman addini dake jihar, inda ta gargadesu kan su ja kunnen mabiyansu wajen kaucewa daukar doka a hannu.

Karin labarai:

Baba Impossible ya musanta fatawar da Maigida Kacako ya bayar

Kowa yazo ya dauki dan sa daga makarantun Mari ko mu dauki mataki –Gwamnatin Kano

Continue Reading

Labaran Kano

Mun daina karbar masu laifi -Gidan yarin Kano

Published

on

Jami’an hukumar ajiya da gyaran hali ta kasa reshen jihar Kano, sun ki amincewa su karbi masu laifi da kotu ta tura musu a yau Laraba.
Masu laifin wadanda kotun majistret dake unguwar Gyadi-gyadi a nan Kano ta yankewa hukunci ta kuma bada umarnin a kaisu gidan ajiya da gyaran halin, sai dai mahukunta gidan sun ki amincewa su karbi masu laifin.
Freedom Radio ta tuntubi kakakin hukumar ajiya da gyaran hali ta kasa reshen jihar Kano, DSC. Musbahu Lawal Kofar Nassarawa wanda ya ce, hukumar su ta samu wata oda daga sama, wadda ta dakatar dasu daga karbar duk wani mai laifi, har sai zuwa bayan annobar Coronavirus.

Karin labarai:

Wasu matasa sun yi kokarin shigar da kwaya gidan yarin Kano

Kun san dalilan da suka sanya aka garkame Sadiya Haruna a gidan yari?

Continue Reading

Kiwon Lafiya

Wani mutum ya rasu bayan ya killace kansa a Kano

Published

on

Wani magidanci a unguwar Gwammaja dake nan Kano ya rasu, bayan ya killace kansa a gidan sa dake unguwar.

Magidanci da har izuwa yanzu ba a bayyana sunan sa ba, ya killace kansa ne tsawon kwanaki uku bayan ya dawo daga birnin tarayya Abuja.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito mana cewa jami’an ma’aikatar lafiya ta jihar Kano sun hallara a unguwar ta gwammaja dauke da kayayyakin aiki na musamman domin bincike da daukar gawar.

Sai dai Kansilan lafiya na karamar hukumar Dala Ibrahim Garba ya shaidawa Freedom cewa, sakamakon bincike jami’an lafiya ke tsaka da gudanarwa a halin yanzu, nan una cewa mutuwarsa na da alaka da bugun zuciya.

Cikakken labarin zai zo muku a shirin Inda Ranka na yau da karfe 9:30 na dare

Karin labarai:

 An tantance mutane 46 a Kano kan Coronavirus

Covid19: Ana dab da kammala ginin cibiyar killacewa da Dangote ke ginawa a Kano

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 316,595 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!