Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Ana cigaba da yiwa malaman addini bita kan cutar Corona a Kano

Published

on

Kwamitin wayar da kai da hadin gwiwar majalisar limamai da ta malamai ta jihar Kano sun shirya wani taron bita na kwanaki uku domin wayar da kan malamai game da cutar Coronavirus.

Taron bitar wanda ake gudanar dashi a dakin taro na gidan Mumbayya dake nan Kano, a ranakun Laraba 10 goma ga watan Yunin da muke ciki da Lahadi 14 ga watan, zaku ma a kammala ranar Laraba 17 ga watan na Yunin, ya mayar da hankali wajen wayar da kan malamai kan yadda zasu wayar da kan al’umma wajen ganin an dakile wannan cuta.

A yayin taron bitar shugaban kwamitin kula da muhalli na jihar Kano, Kuma kwamishinan muhalli na jihar Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya nemi limamai da su kara kaimi wajen fadakar da jama’a akan wannan cuta ta Covid-19 mai saurin yaduwa.

Dakta Kabiru Getso ya ce yanzu haka gwamnatin Kano ta rabawa masallatai dari biyar kayan kariya daga cutar Corona, kuma ana cigaba da rabawa sauran masallatai.

Hotuna a yayin taron bitar:

A nasa bangaren shugaban kungiyar limamai ta Kano kuma limamin masallacin Jumu’a na Ahmadu Tijjani dake Kofar Mata Sheikh Nasir Muhammad Nasir yace abu ne mai kyau gwamnati ta fadakar da limamai kan cutar ta Corona.

Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito mana cewa daukacin limaman da suka halarci bitar sunyi kira ga gwamnati kan ta basu hadin kai wajen yiwa jihar Kano addu’a dama kasa baki daya.

Yanzu haka dai hukumomi a Kano tuni suka rungumi tsarin yin Rayuwa da Corona ta hanyar sassauta matakan da ake dauka game da cutar.

Ko a ranar Lahadi gwamnatin Kano ta sanar da kara sassauta dokar kulle a jihar inda ta amince da ranar Litinin ta zamo daya daga ranakun da mutanen Kano zasu rima sararawa daga dokar zaman gida, kamar yadda wakiliyar Freedom Radio a fadar gwamnatin Kano Zahra’u Nasir ta rawaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!