Coronavirus
Covid-19: Brazil na cikin tsaka mai wuya
Sama da mutum 30,000 hukumomi a kasar Brazil suka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus a ranar Talata kadai.
Yanzu haka dai kasar ta kasance ta biyu a duniya a yawan masu dauke da Coronavirus.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin kasar, Walter Braga Netto ya ce duk da halin da suka tsinci kansu a ciki suna kokarin shawo kan matsalar.
Mutum sama da 1,200 ne suka mutu a ranar litinin kadai, wanda hakan ya nuna cewa adadin mutanen da suka mutu a Brazil daga lokacin bullar Covid-19 ya haura 45,000.
Ko da yake tun farko shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya nuna adawa da matakan tazara a tsakanin mutane, inda a yanzu haka tuni aka bude kasuwanni da sauran wuraren hada-hada, duk da halin da kasar ke ciki na fama da matsananciyar annobar Covid-19.
You must be logged in to post a comment Login