Connect with us

Labarai

Covid-19: Buhari ya hana jami’an gwammati fita kasashen waje

Published

on

Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya dakatar da ma’aikatan gwamnatin kasar nan daga fita kasashen waje sakamakon bullar cutar Coronavirus.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala wani zama na musamman da majalisar zartarwa ta kasa tayi kan cutar ta Coronavirus, kamar yadda mai taimakawa shugaban kasa akan kafafan sadarwa na zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafin sa na Twitter.

Bashir Ahmad ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa wani kwamiti na musamman wanda ya kunshi mutane goma sha uku, da zaiyi aiki kan magance cutar ta Coronavirus wanda Boss Mustapha zai shugaban ta.

Sai kuma tsohon shugaban hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta kasa Dr. Sani Aliyu a matsayin babban jami’in kwamitin.

*BS.*

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!