Labarai
Covid-19: Buhari zai rabawa al’ummar Kano sama da naira biliyan daya
Gwamnatin tarayya za ta fara rabon kudade da yawan su ya kai Naira Biliyan 1 da milyan 600 ga masu karamin karfi dubu 84 cikin kananan hukumomi 15 na jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan yayi dai-dai da umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa ma’aikatar jin kai da takaita afkuwar ibtila’i ta tarayya kan ta fara raba kudin ga mabukata da kuma masu karamin karfi a fadin kasar nan.
Jami’in da ke kula da shirin rabon kudin Dr.Temitope Sinkaiye ce ta bayyana hakan a yammacin jiya Lahadi lokacin da ta kawo ziyara ga mataimakin gwamnan jihar Kano Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna.
Ta ce cikin wadancan kudade, duk wanda za’a baiwa zai samu Naira dubu 20 wanda za’a fara aikin rabon a yau litinin, a wani bangare na rage radadin da zaman gida ya haifarwa al’ummar kasar nan dalilin cutar Covid-19.
Wata sanarwa da sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar Kano Hassan Musa fagge ya fitar ta bayyana cewa, gwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf wajen ganin rabon kudin ya tafi kamar yadda aka tsara.
You must be logged in to post a comment Login