Connect with us

Coronavirus

COVID- 19 : CBN ta rarraba tsabar kudi Naira biliyan 69

Published

on

Babban bankin kasa CBN ya ce ya rarraba tsabar kudi Naira biliyan 69 cikin biliyan 100 da aka ware don tallafawa dai-daikun mutane da kuma masu kanana da matsakaitan sana’o’I da annobar Covid-19 ta shafa.

Wamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefile ne ya bayyana hakan yau a yayin bikin bude taron kungiyar ma’aikatan banki ta kasa karo na 13 a birnin tarayya Abuja.

Idan dai za’a iya tunawa a baya can babban bankin kasa CBN ya sanar da rabar da naira biliyan 50 ga masu kanana da matsakaitan masana’antu don karfafa jarin su da ya durkushe saboda Cutar Corona, inda aka dora musu kaso biyar a matsayin kudin ruwa.

Emefile ya kuma kara da cewa ‘yan Najeriya da dama sun amfana da wadannan kudade, kuma hakan babban al’amari ne da zai tallafawa talakawa amsu karamin karfi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,772 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!