Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Covid 19- Fitilar Bichi ta raba kayan tallafi

Published

on

Kungiyar cigaban al’ummar Bichi,  Fitilar Jama’ar Bichi, ta raba Robobin wanke hannu, Sabulai, da Sindarin tsaftace hannu ,hade da  takunkumi da sauran kayan daukar matakan kariya daga cutar Corona tare da  bayanai na kare kai daga kamuwa da cutar.

Daga cikin guraren da aka raba kayan sun hada da Asibitin Bichi, gidan gyaran hali wato Kurkuku, Gidan Sarki, da Masallacin  Saye da na  Badume.

Da yake jawabi a yayin bada kayan tallafin , shugaban Fitilar Jama’ar Bichi  Alhaji Rilwanu Idris Malikawa Garu, ya ce tallafin anyi shi ne domin amsa kiran gwamnati na yakar cutar da kuma dakile yadauwar ta.

Labarai masu alaka.

Covid-19: Buhari zai rabawa al’ummar Kano sama da naira biliyan daya

Covid-19: Ban san me ya hada 5G da Coronavirus ba – Pantami

Rilwanu Idris Malikawa Garu, ya  da da da cewa kungiyar zata kuma yi makamancin wannan rabon, a cikin karshen mako a yankin  Danzabuwa, tare da yin addu’ar Allah ya kawo karshen wannan Annoba, da baiwa wanda suka kamu da cutar lafiya.

A nasa jawabin mataimakin Darakta na Asibitin Bichi, Alhaji Muhammad  Abdullahi, ya yabawa kungiyar bisa kokarin da suke a yankin na Bichi, don ganin cigaban yankin da tallafwa marasa galihu.

Muhammad Abdullahi, ya yi kira ga al’umma dasu guji zuwa Asibitoci domin duba marasa lafiyar da ka kwantar, don gudun yada cututtuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!