Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19 Dalglish ya kamu da cutar Corona

Published

on

Gwarzon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, kuma tsohon mai horar da kungiyar Kenny Dalglish, ya kamu da cutar ya kamu da cutar Corona.

Mai shekaru 69, Dalglish, wanda yake tsohon dan wasan gaba ne na  kasar Scotland  ya fara wasa a kungiyar Celtic dake kasar Scotland, ya fara nuna alamun cutar ne a ranar Jumma’a kamar yadda iyalin sa suka bayyana.

An kai gwarzon dan wasan na Liverpool Asibiti ne, ranar Larabar data gabata sakamakon yanayin rashin lafiya, sai dai tun kafin a kaishi Asibitin, dan wasan ya killace kansa da iyalin sa a gidan sa.

Labarai masu alaka.

DA DUMI-DUMI: Sadio Mane ya lasher kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afrika

Hanyar da Diago Simeone ya bi wajen fitar da Liverpool a Champion

Dalglish, ya dau gasar kasar Scotland da kungiyar Celtic, har sau hudu kafin komawar sa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a shekarar 1977, inda ya lashe gasar kasar Ingila sau takwas.

Kazalika dan wasa Kenny Dalglish, ya lashe kofin kalubale na FA, har sau uku da kofin nahiyar turai shima sau uku da kungiyar ta Liverppol, tuni dai kungiyar da dumbin magoya bayanta  a fadin duniya suka aike da sakon alhini da taya shi addu’ar samun lafiya daga cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!