Connect with us

Labarai

Covid -19 Ba za’a rage albashin ‘yan wasan firimiya ta kasa ba

Published

on

Kungiyoyin dake buga gasar Firimiya ta kasa zasu cigaba da karbar albashin  su ba  tare da zabtare ko rage wani kaso a cikin sa ba kamar yadda aka dinga rade radi a baya.

Rahotanni a baya na ta kewaya wa cewar akwai yiwuwar zabtare albashin wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyoyin dake taka leda a kasar nan, tun bayan bullar cutar Corona Virus, a fadin duniya wanda hakan ya sa wasu kungiyoyi da ‘yan wasa da dama a nahiyar turai da sauran kasashe rage kudaden gudanar da su tare da rage yawan ma’aikata duba da halin da ke ciki.

Labarai masu alaka.

An fidda alkaluman gasar firimiya ta kasa zuwa wasannin mako na ashirin da biyu

Anyi garkuwa da ‘yan wasa biyu a Firimiyar Najeriya

Hakan tasa ‘yan wasa a kasar nan fargabar rage musu albashi kasancewar mafiya yawan kungiyoyin gwamnatocin jihohi ne ke daukar nauyin su.

A baya dai kungiyar kwallon kafa ta Yobe Desert Stars, ta rage yawan alabashin ‘yan wasanta dana ma’aikatan kungiyar da kaso saba’in da biyar cikin dari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!