Coronavirus
Covid-19: Ganduje ya amince a gudanar da sallar idi a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta sahale a gudanar da sallar idi bisa wasu sharuda kamar yadda mai taimakawa gwamnan Kano kan yada labarai Salihu Tanko Yakasai ya shaidawa Freedom Radio.
Za a yi amfani da tazara wajen gudanar da sallar a ranar idin
An kafa kwamiti na musamman da ya kunshi bangarorin malamai da na gwamnati domin tabbatar da cewa an bi matakan da gwamnati ta gindaya.
Dole ne ayi amfani da takunkumin rufe fuska.
Babu batun bukukuwan sallah, saboda haka da zarar an kammala sallar idi, dokar kulle zata cigaba da aikinta.
Labarai masu alaka:
Covid-19: Ganduje ya amince a cigaba da sallar juma’a a Kano
Covid-19: Buhari ya tsawaita dokar kulle a Kano
Tun bayan bullar cutar Covid-19 gwamnan Kano abdullahi Umar Ganduje ya sanya dokar zama a gidan tsawon mako guda, daga bisani ya kara sati biyu.
Sai dai bayan da satin biyun ya cika wa’adi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya dokar kulle har tsawon mako biyu a jihar Kano.
A ranar 11 ga watan Mayun 2020 ne dokar gwamnatin tarayya ta cika wa’adi, sai dai kuma gwamnatin Kano ta tsawaita ta zuwa mako guda.
Ranar 18 ga watan Mayun 2020 ne kwamitin kar ta kwana na fadar shugabacin kasa kan annobar Covid-19 karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya sanar da cewa na tsawaita dokar kulle a jihat Kano ta tsawon mako biyu.
Ko da yake hakan be hana gwamnatin Kano yanke shawarar bayar da dama a gudanar da sallar juma’a da kuma idi ba, bisa sharuddan da suka kunshi bayar da tazara da kuma amfani da takunkumin rufe fuska dole.
You must be logged in to post a comment Login