Connect with us

Coronavirus

Covid-19: Ganduje ya amince a cigaba da sallar juma’a a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta amince a cigaba da sallar juma’a a Kano, amma za’a cigaba da bin dokar lockdown a ranar ta juma’a.

Gwamnan Kano abdullahi Umar Ganduje ne ya amince da hakan a yayin ganawar da yayi da malaman addinai a fadar gwamnti.

Me taimakawa gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Salihu Tanko Yakasai ya tabbatarwa da freedom radio cewa iya sallar juma’a za’a rika gudanarwa a ranar, sakamakon wasu sharudda da suka kunshi bada tazara da kuma hana cakuduwar jama’ar.

A cewar Tanko Yakasai gwamnatin Kano ta shirya rabawa masallatan takunkumin rufe fuska.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,103 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!