Connect with us

Labarai

Covid-19: Ganduje ya bada umarnin rufe makarantun firamare da sakandire

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rufe daukacin makarantun firamare dana sakandare dake fadin jihar.

Kwamishinan ilmi na jihar Kano Alhaji Sanusi Muhammad Sa’id ne ya bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai.

Ya ce matakin ya zama wajibi don zama kandagarki kan cutar Corona dake ci gaba da yaduwa.

Kwamishinan ilmi Alhaji Sanusi Muhammad Sa’id  ya kara da cewa, hutun zai kasance na makwanni hudu, wanda daga bisani Gwamnatin Kano za ta duba matakin dauka na gaba.

Wakilin mu Umar Idris Shuaibu ya ruwaito gwamnatin jihar Kano ta bukaci iyaye da su sanya ido wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yan su, tare da nusar da su muhimmancin kula da tsaftace hannayen su akai-akai, don kiyaye lafiyar su da ta al’umma gaba daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!