Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Ganduje ya bada umarnin rufe wasu makarantun gaba da Sakandire

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin rufe wasu cikin makarantun gaba da Sakandiren jihar nan take.

Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishiniyar ilimi mai zurfi ta jiha Dr. Mariya Mahmud Bunkure ta fitar.

Makarantun da aka rufe sun haɗar da, Kwalejin share fagen shiga jami’a ta Rabi’u Musa Kwankwaso da ke Tudunwada.

Sai kuma Kwalejin nazarin tsaftar muhalli da ke garin Gwarzo, da kuma ta fasahar bunƙasa sana’o’in dogaro da kai da ke garin Rano.

Rufewar ta kuma shafi Kwalejin nazarin harkokin noma ta garin Ɗanbatta.

Labarai masu alaka:

Tsaro: Ganduje ya bada umarnin rufe makarantun kwana cikin gaggawa

Corona: El-rufa’i ya bada damar buɗe ƙarin makarantu da Islamiyoyi

Ta cikin sanarwar Kwamishiniyar ta ce, an ɗauki wannan mataki ne sakamakon shawarwarin da aka bai wa Gwamnati, ɗalibai su gaggauta koma wa zuwa gida nan take.

Idan hali ya yi, Kwamishiniyar ta ce, za a sanar da ranar ci gaba da karatun.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Gwamnatin jihar ta bada umarnin rufe wasu makarantun Sakandiren kwana goma da ke jihar.

A sanarwar da Kwamishinan ilimin Kano Malam Sanusi Sa’idu Ƙiru ya fitar a ranar Juma’a ya ce, an ɗauki matakin ne saboda dalilan tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!