Coronavirus
Covid-19: Ganduje ya caccaki rahoton gwamnatin tarayya kan mace-macen Kano
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya caccaki rahoton gwamnatin tarayya da ta fitar game da mace-macen da aka yi a Kano.
Maitaimakawa gwamnan kan kafafen sada zumunta, Abubakar Aminu Ibrah ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.
Cikin rahoton da kwamitin tarayya ya fitar ranar Litinin, ta bakin ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire ya ce mutum 979 da suka mutu a wancan lokacin cikin kananan hukumomin jihar Kano takwas, na da cikakkiyar alaka da cutar COVID-19.
Dakta Ehanire ya ce shakka Babu bincikensu ya tabbatar cewa kashi 50 zuwa 60 na mace-macen a jihar Kano ya faru ne sakamakon Coronavirus wadda yanzu haka ta kama mutum fiye da dubu guda a jihar.
A watan Afrilun da ya gabata ne aka samu mace-mace a jihar Kano, abinda yafi kamari a kan masu tsawon shekaru, lamarin da aka rika zargin hakan na da alaka da cutar Coronavirus.
A wancan lokacin kwamitin karta kwana kan yaki da annobar Covid-19 na tarayya, ya danganta mace-macen da annobar Covid-19, kamar yadda binciken su ya tabbatar.
Ko da yake a wancan lokacin, gwamnatin Kano ta musanta cewa mace-macen na da alaka da annobar Covid-19, abinda ta ce shine, wasu nau’in cutuka ne da suka danganci hawan jini, ciwon sukari da dai sauran su.
You must be logged in to post a comment Login