Labarai
Covid-19: Gwamnatin tarayya ta bada umarnin bayar da tallafi ga mabukata
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba umarnin fadada shirin ba da tallafi ga al’ummar kasar nan don rage musu radadin da suke ciki sakamakon ci gaba da yaduwar cutar corona.
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a jiya yayin wani jawabi da ya gabatarwa al’ummar kasar nan.
A cewar shugaban kasar, tuni ya ba da umarnin fadada yawan marasa galihu wadanda za su ci gajiyar tallafin da gwamnati ke bayarwa daga mutum miliyan biyu da dubu dari shida zuwa mutum miliyan uku da dubu dari shida cikin makwanni biyu masu zuwa.
Ya ce, daukar wannan matakin ya zama wajibi don ragewa marasa galihu radadin da za su shiga sakamakon ci gaba da yaduwar cutar covid-19.
Muhammadu Buhari ya kuma bai wa ministocin ma’aikatun masana’antu da kasuwanci da zuba jari da na sadarwa da kimiyya da fasaha da ministan sifiri da takwaransa na zirga-zirgar jiragen sama da kuma minintarn cikin da su bullo da sababbin tsare-tsare da za su taimaka wajen ganin tattalin arzikin kasar nan na tafiya kan yanayi mai kyau.
Sauran sune ministocin ma’aikatun lafiya da ayyuka da gidaje da kwadago da samar da aikin yi da kuma na ilimi da su yi hadin gwiwa wajen gudanar da ayyukan da za su taimakawa walwalar al’ummar kasar nan.
Haka zalika shugaba Buhari ya kuma bai wa ma’aikatar aikin gona da raya karkara da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da ofishin Majalisar samar da isasshen abinci ta kasa da kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan samar da takin zamani da su yi aiki tare da kwamitin shugaban kasa kan dakile illar cutar ta covid-19 da nufin dakile illar da cutar covid-19 ka iya yiwa harkokin manoma.
You must be logged in to post a comment Login