Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Covid-19: Kungiyar mata ‘yan jaridu ta dage taronta na shekara

Published

on

Kungiyar mata ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano ta dage taron da kungiyar zata gudanar a ranar Asabar mai zuwa sakamakon cutar Corona.

Shugabar kungiyar anan Kano Hajiya Bilkisu Ado Zango ce ta sanar da hakan ga manema labarai da yammacin yau Alhamis cewa ya zama wajibi kungiyar ta dage taron da ta shirya gudanarwa a ranar Asabar 21 ga wannan watan da muke ciki.

A cewar Hajiya Bilkisu Ado Zango a halin da ake ciki babu taro sai abinda hali yayi, kasancewar Gwamnatin Kano na daukar matakai wajen barkewar cutar ta COVID-19 a nan Kano.

Shugabakar kungiyar ta kara da cewar da zarar an sanya ranar za’a sanar da manbobin kungiyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!