Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Kungiyar P4CS ta bukaci gwamnatin tarayya ta tallafawa jihar Kano

Published

on

Kungiyar hadin kai da kare al’umma wato Partners for Community Safety, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kwamitin karta kwana na yaki da cutar Corona da Ministan Lafiya na kasa da kuma masu ruwa da tsaki a kasar nan da su zo su tallafawa jihar Kano da kayan aikin gwajin cutuka masu yaduwa musamman a wannan lokaci da ake fama da cutar Corona.

Shugaban kungiyar, Kwamared Ali Wali ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai game da yadda cutar Corona ke kara yaduwa a jihar Kano.

Ya yi kira ga hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC kan ta samar da karin cibiyoyin gwajin cutar Corona a Kano la’akari da yadda jihar ta Kano ke da dumbin mutane.

Kwamred Ali Wali ya kuma bukaci gwamnati da ta gudanar da aikin gwaje-gwajen cutuka ga al’ummar jihar Kano.

Munaneman a kara mana cibiyoyin gwajin Corona a Kano-P4CS

Ya kuma bukaci gwamnati da ma’aikatar lafiyar ta kasa da ta samar da kayan aiki ga Asibitocin dake jihar Kano domin karfafawa ma’aikatan lafiya damar gudanar da aikin su yadda ya kamata.

A kwanakin baya dai kungiyar ta Partners for Community Safety, ta gudanar da taro makamancin wannan, inda ta bukaci gwamnatin tarayya ta samar da karin ciboyiyin gwajin cutar Corona a jihar Kano.

Tare da yin kira ga hukumomin tsaro kan su kara zage dantse wajen gudanar da ayyukan su na hana shige da fice a jihar Kano, duba da yadda har yanzu ake samun wadan da ke shigowa jihar ta Kano ta barauniyar hanya.

Harma yai kira ga al’umam da malamai da shugabanni kan su baiwa gwamnati hadin kan da ya kamata domin ganin an magance cutar ta Corona a Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!