Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Covid-19: Mutane 10 sun kara kamuwa a jihar Legas

Published

on

Hukumar kula da cututtuka ta kasa NCDC ta ce mutane  goma ne suka sake kamuwa da cutar Covid-19 a jihar Legas.

Hukumar ta bayyana hakan ne a daren talata a shafinta na Twitter, inda ta ce yanzu masu dauke da cutar a jihar Legas sun karu daga 120 zuwa 130.

Haka ma a birnin tarayya Abuja wadanda suka kamu da cutar sun karu zuwa guda 50 sakamakon samun Karin mutum 2 dake dauke da cutar.

LABARAI MASU ALAKA

Covid-19: Mutane 2 sun warke a jihar Legas

Covid-19: An kara samun mutane 6 sun kamu a Najeriya

Covid-19: An tsawaita hutun kotunan kasar nan

Rahotanni sun yi nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake nazarin rufe birinin tarayya Abuja kafin karshen wannan satin bayan ya yi bibiya ga yadda cutar ta Corona ta shafi al’ummar kasar nan.

Sakataran Gwamnatin tarayya Boss Gida Mustapha ne ya bayyana haka lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi akan halin da ake ciki na cutar Corona a jihar Legas.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!