Labarai
Covid-19: NYSC ta dakatar da aikin mako-mako na ‘yan hidimar kasa
Hukumar kula da masu yiwa kasa hidima ta kasa NYSC ta ce ta dakatar da gudanar da aikin nan na al’umma da matasa ‘yan bautar kasa ke yi mako-mako wato CDS a wani bangare na dakile yaduwar cutar coronavirus da aka samu bullarta a kasar nan.
Rahotanni sun bayyana cewa an rufe dukkannin sansanin ‘yan gudun hijira da ke fadin kasar nan.
Batun dakatar da aikin na CDS na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar Abdulrazak Salawu, inda yace an dauki wannan mataki ne don dakile yaduwar vutar ta Corona.
Hukumar NYSC ta gargadi Hukumomin Jami’o’in Najeriya
Unpaid allowances: Corps members stage protest, disrupt NYSC POP in Kano
Kamar dai yadda ya ke bisa ka’ida ‘yan bautar kasa na taruwa guri guda don gudanar da ayyukan al’umma duk mako, wanda hakan kuma na tara jama’a da dama.
Sanarwar ta kuma bukaci dukannin shugabannin hukumar da ke kula da kananan hukumomi da su yi biyayya ga wannan umarni.
You must be logged in to post a comment Login