Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Sanya “Face Mask” ya zama dole a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta umarci kotun tafi da gidanka kan ta rika hukunta duk wadanda aka kama basa sanya takunkumin fuska don kariyar cutar Corona.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yau lahadi lokacin da kwamitin kar ta kwana kan cutar Corona ke bayyana halin da Kano ke ciki kan cutar.

Ya kara da cewa domin dai kariyar alummar Kano daga cutar gwamnatin ta ke raba takunkumin kyauta a kananan hukumomi 44 da ke jihar ta Kano

Da yake jawabi Babban jamiin Kwamitin Kar ta akan cutar Corona Dr Tijjani Hussain yace ya zuwa yanzu an sallami mutum 32 da suka warke daga cutar.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa Gwamnan a yau ya kuma ziyarci makarantar horar da masu wasanni dake karfi wacce zaa mayar da ita cibiyar killace masu Corona da kuma Inda ake yiwa jamian lafiya horar wa a Kura kan cutar.

Karin labarai:

Ganduje ya rabawa likitoci kayan kare kai daga Corona

Za a rika bude Kano sau biyu a sati -Ganduje

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!