Coronavirus
Ganduje ya rabawa likitoci kayan kare kai daga Corona
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci asibitoci masu zaman Kansu dasu daina mayar da marasa lafiya gida idan sun zo asibitocin su.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake zagayawa asibitoci masu zaman kansu yana raba kayan kariyar jamian lafiya da feshin magani.
Gwamna Ganduje ya kara da jan hankalin su akan su yi amfani da kayan kariyar Don kariyar kansu da kuma sanar wa da gwamnatin duk wanda aka Gani yana da alamun Corona
Karin labarai:
Yanzu-yanzu: Ganduje ya fara rabon tallafin Corona
Za a rika bude Kano sau biyu a sati -Ganduje
Da yake jawabi shugaban tawagar kwamitin ministan lafiya a Kano Dr Nasir Sani Gwarzo lokacin da Gwamnan ya ziyarci inda kwamitin ke horar da jamian lafiya ya ce a yanzu haka sun gano matsalar Kano kan cutar Corona kuma suna dab da cimma nasara.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa asibitocin da Gwamnan ya ziyarta don kai tallafin Kayan kariyar da kuma feshin magani sun hada da Asibitin idanu na Makka da asibitin Al’amin medical center da asibitin Standard specialist hospital.
You must be logged in to post a comment Login