Connect with us

Labarai

Za a rika bude Kano sau biyu a sati -Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata rika bude gari a lokacin nan na zaman gida a duk ranar litinin da alhamis daga karfe goma na safe zuwa hudu na yamma kowacce rana.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a yau asabar da yake zantawa da manema labarai.

Ya kuma ce ba za a bude kasuwanni ba sai dai kasuwannin Yanlemo da Yan kaba ne kadai aka yadda su bude suma daga karfe goma na safe zuwa hudu na yammar kowacce litinin da alhamis din ranakun.

Ya kuma kara da cewa Alhaji Aliko Dangote ya Samar da cibiyar gwajin cutar ta tafi da gidan ka da zata rika gwada mutane Dari hudu kowacce rana.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa mataimakin Gwamnan Nasir Gawuna yace za a Samar da cubiyoyin gwajin cutar Corona nan bada dadewa ba a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!