Labarai
COVID-19 : UNICEF na ziyartar makarantu a Kano
Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya wato Unicef ya fara ziyartar makarantun Firamare dake fadin jihar Kano domin duba kayayyakin kariya na Covid 19 da suka rabawa makarantun Firamare.
Sakataren Ilimi na asusun tallafawa kananan yara dake aiki a Najeriya Nasaka Adebayo Ibrahim ya bayyana hakan yin da suka kai ziyara karamar hukumar Kunchi.
Nasaka Adebayo Ibrahim ya ce sun fara kai ziyarar ne domin tabbatar da makarantun furamare suna kiyaye dokar Corona musamman ma a yankin karkakar
Yace sun raba abubuwan wanke hannu a makarantun Firamari bisa duba adadin yawansu domin tabbatar da an dakile yaduwar cutar Corona a tsakanin dalibai.
Malam Mati Sha’aibu guda ne daga cikin malaman makaranta ana Kano yace iyayen yara basa son turo yara su makaranta sai dai su turasu kasuwa.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin makarantun suna bukatar malamai da kayayyakin koyo da koyarwa .
You must be logged in to post a comment Login