Labarai
Covid-19: Yadda masu zuba jari suka yi asarar biliyoyin kudi a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe sansanonin masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan, a wani bangare don dakile yaduwar yaduwar annobar cutar Corona.
Ministan matasa da wasanni Sunday Dare ne ya bayyana hakan a safiyyar Yau.
Jaridar Punch ta rawaito cewa ministan ya kuma ce za su sallami wadanda suke cikin sansanonin yiwa kasar hidima a halin yanzu domin komawa garuruwan su.
A cewar ministan hakan ya biyo bayan sabon tsarin da gwamnatin tarayya ta dauka na dakile yaduwar cutar Corona a fadin kasar nan.
Rahotanni sun bayyana cewa tuni rukunin farko na wannan shekarar suka shiga sansanonn a ranar hudu ga wannan watan kuma za su fito a ranar Ashirin da tara ga wannan watan.
You must be logged in to post a comment Login