Connect with us

Labarai

Covid-19: Za a tallafawa malaman Islamiyyu a Kano

Published

on

Wata kungiyar cigaban al’umma mai suna Crown Youth Initiative dake nan Kano, tace ta shirya tsaf domin bata tallafi ga malaman makarantun Islamiyyu dake Kano, sakamakon halin rufe makarantu da gwamnati tayi saboda annobar Coronavirus.
Shugaban kungiyar Kwamaret Usman shine ya bayyana hakan, yayin wata ziyara da suka kawo Freedom Radio a yau.


Kwamaret Usman Muhammad Yaro ya ce ganin yadda malaman Islamiyya ke cikin mawuyacin hali, ya sanya kungiyar ta ga dacewar tallafa musu domin rage musu radadin zama a gida.
Idan zaku iya tunawa dai, a makon da ya gabata ne wasu malaman Islamiyya suka garzayo shirin Inda Rank ana Freedom Radio inda suka kuka kan mawuyacin halin da suke ciki, tun bayan rufe makarantu da gwamnatin Kano ta bada umarni.
Malaman Islamiyyar sun ce, sun shiga cikin halin ha’ula’I kasancewar da kudin laraba suka dogara.

Karin labarai:

Covid-19: KAROTA ta gargadi masu shirin taron daurin aure

Covid 19: Gwamnatoci su kara kokari-Dakta Muhammad Abdu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!