Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Covid -19:Borna Coric ya kamu da Corona

Published

on

 

Dan wasa Borna Coric, ya bayyana kamuwa da cutar Corona , kwana guda bayan da aka soke gasar Andria Tour dalilin kamuwar Grigor Dimitrov , da kamuwa da cutar.

Coric , ya bayyana haka ne a shafin sa na Twitter , inda ya ce ina mai alhinin shaida muku cewar na kamu da cutar Corona.

Ina kuma kira ga duk wanda mukayi mu’amala daya kai kansa a gwada shi don tabbatar da lafiyar sa, da fatan zaku yafe min inji Coric.

Labarai masu alaka.

Za’a dawo gasar wasan Tennis ta US Open a bana ba tare da ƴan kallo ba

An dakatar da wasan Tennis saboda barazanar cutar codiv 19.

Jim kadan bayan, bayyana hakan dan wasa Nick Kirgyios , ya soki gundanar da gasar inda yace hakan ke kasancewa ga duk wanda ya ki bin ka’idoji, ina muku fatan samun lafiya.

Gasar Andria Tour , dan wasa Novak Djokovic ne ya shirya ta , a kasar Serbia da Croatia don habbaka tare da dawo da karsashin ‘yan wasa kafin dawowa sauran manyan gasa ta duniya da ake sa ran gudanar da su daga karshen watan Agustan bana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!