Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Covid -19:Masari ya Dakatar da wasanni da gidajen kallo a Katsina

Published

on

 

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya bayyana tare da jaddada hana harkokin wasanni a jihar tare da gidajen kallon su sakamakon cutar Corona.

Sanarwar ta fito ne wacce aka rabawa manema labarai daga ,ma’aikatar wasanni ta jihar mai dauke da sa hannun Nalado Iro.

Labarai masu alaka.

COVID-19: Ma’aikata za su koma aiki a Katsina

Katsina United ta musanta rashin biyan ‘yan wasa albashi

Sanarwar ta kara dacewa , ma’aikatar ta lura da karya dokar da wasu suke ta hanyar dawowa gudanar da harkokin wasanni da gidajen kallon , wanda hakan ya saba karara da dokar gwamnatin tarayya na takaita zirga zirga da mu’amala dangane da cutar Corona.

Don haka sanarwar , take gargadin masu yi fa cewar zasu fuskanci doka , kuma al’umma su sani har yanzu Kwallon kafa , wasannin motsa jiki da gidajen kallo duk an haramta su da gudanar da su a jihar har zuwa wani lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!