Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Covid -19:Yanzu -Yanzu Djokovic ya kamu da Corona

Published

on

 

Dan wasa na daya a duniya a wasan Tennis Novak Djokovic , ya bayyana sanar da cewar ya kamu da cutar Corona sakamakon gwajin da akayi masa.

Mai shekaru 33, Djokovic ya kasance dan wasa na uku da ya kamu da cutar bayan Grigor Dimitrov da Borna Coric , duk a sakamakon wasan gasar Andria Tour da Djokovic ya shirya don samun Karin kuzari da motsa jikin ‘yan wasa bayan dogon hutu da cutar ta Corona ta haddasa na dakatar da wasanni.

Novak Djokovic , ya bayyana hakan ne a shafin Instagram na gasar Andria tour, inda ya ce shi da matar sa Jelena sun kamu da cutar , amma yaran su basu da cutar.

Labarai masu Alaka.

Covid -19:Borna Coric ya kamu da Corona

Za’a dawo gasar wasan Tennis ta US Open a bana ba tare da ƴan kallo ba

Djokovic , ya bada hakuri tare da rokar al’umma gafara inda ya kara dacewa sun shirya gasar ne da zuciya daya, tare da neman kudin da zamu bada gudunmowa ga mabukata bisa tsare tsaren lura da lafiya ganin cewar cutar anci karfin ta, sai kuma gashi abinda ya biyo baya.

Shima dan wasa Victor Troiki da ya yi wasa a gasar da matar sa sun kamu da cutar.

A baya bayan nan dai ‘yan wasa irin su Nick Kyrgios da Dan Evans da Andy Murray , sun soki tsarin gudanar da gasar , inda Andy Murray yace yana fata hakan zai zama darasi garemu da kowa da kowa.

Novak Djokovic , ya ce zai killace kansa na makwo biyu , tare da yin gwaji har tsawon kwana biyar don karbar maganin na Annobar da ta mamaye duniya a yanzu haka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!